Yan Sanda Sun Dakatar Da Kama Motoci Masu Duhun Gilasai

Spread the love

Rundunar ‘yansandan Najeriya ta dakatar da aiwatar da dokar kama wadanda ba su da takardar izinin sanya gilashi mai duhu a motarsu, sakamakon umarnin da wata kotu ta bayar kan a dakatar.

Mai magana da yawun rundunar ‘yansandan ta babban birnin tarayya Abuja, SP Josephine Adeh, ne ta bayyana haka a lokacin wata tattaunawa da tashar talabijin ta AIT a yau Laraba.

Ta tabbatar da hakan ne bayan da ta ce a hukumance ‘yansanda sun samu umarnin kotun na dakatar da aiwatar da dokar.

SP Adeh ta ce zuwa yanzu za su bi umarnin kotun har zuwa lokacin da za ta yanke hukunci a kan karar.

Da take magana a kan dalilinsu na kamen masu bakin gilashin wadanda ba su da izini ta ce, an dauki matakin ne saboda matsalar tsaro.

Ta ce wasu na sanya bakin gilashin motarsu su rika aikata miyagun laifuka, wanda hakan ke sa da wuya a iya gane wadanda ake zargi da aikata laifi.

Haka kuma ta yi watsi da zargin da ake yi cewa an bullo da matakin ne domin samun kudi inda tace duk kudin da ake biya na izinin sanya gilashin mai duhu yana shiga asusun bai daya ne na gwamnatin tarayyar Najeriya, amma ba wajen ‘yansanda ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *