Yan Sanda Sun Fara Bincike Kan Magidanci Da Ya Yi Yunkurin Shigar Da Tabar Wiwi Gidan Gyaran Hali A Kano.

Spread the love

Jami’an hukumar gidan ajiya da gyaran hali da tarbiya na Kurmawa Kano, sun samu nasarar cafke wani mutum mai suna Hamisu Mamuda, mai shekaru 51 dake zaune a Unguwar Samegu Karamar hukumar Kumbotso, lokacin da yake yunkurin shigar da tabar Wiwi kulli 12 a Ledoji don siyar wa Daurarru.

Kakakin rundunar Yan Sandan Jahar Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ne ya bayyana hakan ta cikin Wata sanarwa da ya aike wa da jaridar idongari.ng, a Ranar Litinin.

SP Abdullahi Kiyawa, ya ce , yanzu haka Wanda ake zargin yana hannunsu a Babban sashin gudanar da binciken manyan laifuka na CID don fadada bincike akansa.

Kakakin yan sandan ya Kara da cewa, sun samu kiran gaggawa ne daga gidan ajiya da gyaran hali da tarbiya, na Kurmawa Kano, kan cewa an Kama magidanci da kullin tabar Wiwin , a daidai lokacin da jami’an gidan ajiya da gyaran halin ke bincikarsa.

Bayan Samun rahotanne Kwamishinan yan sandan Jahar Kano, CP Muhammed Usaini Gumel, ya tura dakarun yan sanda wadanda suka taho dashi.

Wanda ake zargin ya tabbatar da cewa tabar Wiwi ce wadda ya yi yunkurin shiga da ita gidan domin siyar wa daurarru.

Rundunar Yan Sandan Kano, ta yaba wa ma’aikatan gidan ajiya da gyaran hali da tarbiya, sakamakon namijin kokarin da suka yi har suka Kama shi, a kokarin su na gyaran tarbiyar daurarru amma wasu na kokarin kawo tasgaro.

Kwamishinan Yan Sandan Jahar Kano, CP Muhammed Usaini Gumel, ya bayar umarnin gudanar da cikekken bincike a CID, kuma da zarar an kammala za a gurfanar da shi a gaban kotu don ya fuskanci hukunci.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *