Yan Sanda Sun Gaiyaci Harrison Gwamnishu Kan Wallafa Batan Mutane A Anambra.

Spread the love

Rundunar yan sandan jihar Anambra, ta gayyaci wani mawallafi , mai suna Harrison Gwamnishu, domin ya yi bayani kan wani rahoto da ya wallafa game da batan wasu mutane a jihar.

Mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar, SP Tochukwu Ikenga, ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da ya fitar a jiya asabar a Awka.

Ikenga ya ce Gwamnishu ya wallafa wani labari da cewa mutane biyar sun bace yayin da suke kokarin samun masauki a wani otel dake jihar, said ai rundunar ta ce bata samu korafi a hukumance ba ko wata shaida da ta tabbatar da lamarin.

Rundunar ta bayyana damuwarta kan rashin sahihancin rahotan, shi yasa suka gayyaci mawallaafin jaridar.

Ikenga ya ce rundunar ta fitar da wata sanarwa a ranar Juma’ar data gabata, inda ta bukaci ’yan uwa ko dangin wadanda sun ake zargin bace da su zo su yiwa rundunar bayani na gaskiya.

 

Ya kuma bayyana cewa ,Gwamnishu, ya yi martani a shafin Facebook na rundunar inda ya ce: “Na gode, yan uwansu za su kawo muku rahoton yau’’

Sai dai duk da wannan martani, Ikenga ya ce babu wata nasara da aka samu wajen ganin Gwamnishu ya kawo dangin wadanda ake zargin sun bace.

“Wannan labari mai tayar da hankali ya sa wasu daga cikin mabiyanmu suna tambayar ingancin aikin rundunar ‘yan sanda da sauran hukumomin tsaro, duk da cewa ana zaune lafiya a jihar a yanzu,” in ji Ikenga.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *