Rundunar yan sandan jihar Kano, ta kama wani matashi mai suna, Usman Sagiru, dan Shekaru 20 nazaunin unguwar Sharifai , bisa zargin da da halaka jami’in bijilanti da Kuma raunata wani .
Kakakin rundunar ƴan sandan jihar Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ne ya bayyana hakan a yau Lahadi.
Sanarwar ta ce lamarin ya faru ne, lokacin da tawagar mai martaba sarkin Kano, Muhammadu Sunusi ii, suke dawo wa daga hawan sallar idin karamar sallah da misalin karfe 12:40pm na rana.
Sanarwar ta kara da cewa Wanda ake zargin da wasu mutane da ba a Kai ga gane ko waye ba, sun farwa jami’an bijilanti biyu, Inda suka sokawa Surajo Rabi’u wuka, Wanda hakan ya Yi sanadiyar rasa ransa, sannan sun raunata wani jami’in bijilantin Mai suna Aminu Sulaiman Kofar Mata .
Rundunar yan sandan ta ce yanzu haka ta fara gudanar da bincike kan lamarin.
Haka zalika rundunar ta gaiyaci shamakin Kano, Alhaji Wada Isiyaku, don gudanar da bincike akansa.
Sanarwar ta kara jaddada cewa duk Wani Abu da ya danganci hawan sallah a fadin jihar an haramta gudanar dashi da kuma aiyukan daba.
SP Abdullahi Kiyawa, ya ce duk Wanda aka kama ya dauko Wani Abu ko Yunkurin tayar da hankalin al’umma za a kama shi Kuma doka zata Yi aiki akansa.
A karshe Rundunar ta Yi kira ga al’umma Da su basu hadin Kai don gannin an gudanar da bukukuwan sallah lafiya.