Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Gombe, Hayatu Usman, ya yi gargaɗi ga al’umma kan tsaron taransfominin wutar lantarki, musamman yayin da ake fama da yawan rashin wutar.
Kwamishinan ya jaddada buƙatar a kula da tsaron taransfomomin saboda sun fi fuskantar barazanar sata a lokacin da wuta ta ɗauke.
A cikin wata sanarwa da kakakin kundunar, ASP Buhari Abdullahi, ya sanya wa hannu, CP Usman ya bayyana cewa rashin wuta na bayar da dama ga ɓarayi saboda yawan mutane na raguwa, kuma akwai tunanin cewa na’urorin sun daina aiki.
Wannan yanayi na ba wa ɓarayi damar kai hari kan taransufoma da sauran kayayyakin lantarki.
Kwamishinan ya shawarci al’umma da su dauki matakan tsaro yayin da babu wuta, inda ya ce ya dace a karfafa tsaro da yawaita sintiri ko shirya tsaro na wucin gadi.
Sai ya yi kira ga mutane da su kara kula da taransfommin su yayin da aka sanar da rashin wuta ko a lokutan da aka dade ba a samu wuta ba.
Haka kuma ya shawarci al’ummomin da ke cikin hadarin sata da su tsara tsaron wucin gadi don lura da muhimman wuraren har sai an dawo da wutar.
Kwamishinan ya bukaci al’umma su sanar da makwabta ko kasuwanni da ke kusa da su kasance cikin shiri don lura da duk wani abu mai kama da laifi a kusa da taransfoma.