Yan Sanda Sun Gargadi Jama’a Su Guji Yada Labaran Karya Cewar Sarkin Kano Na 15 Zai Yi Sallah A Kofar Kudu

Spread the love

Rundunar ƴansanda a jihar Kano ta gargaɗi al’umma su guji yaɗa ‘labaran ƙarya’ da ke cewa sarkin Kano da aka sauke Aminu Ado Bayero zai halarci sallar Juma’a a babban masallacin fadar sarki da ke Ƙofar Kudu.

Hakan na ƙunshe ne a wata sanarwa da rundunar ƴansandar ta fitar yau Juma’a, wadda ta samu sa hannun mai magana da yawun rundunar a jihar, Abdullahi Haruna Kiyawa.

A cewar sanarwar ya kamata al’ummar jihar su yi watsi da labaran da ke yawo a shafukan sada zumunta da ke cewa sarkin wanda aka sauke zai halarci sallar Juma’ar a Ƙofar Kudu kasancewar ba gaskiya ba ne.

Haka nan rundunar ta tabbatar da cewa za ta samar da wadataccen tsaro faɗin jihar.

Ana cikin halin ɗar-ɗar a jihar ta Kano tun bayan da Aminu Ado Bayero, wanda gwamnatin jihar ta sauke ya koma birnin na Kano bayan miƙa wa Muhammadu Sanusi II takardar kama aiki a matsayin sarkin Kano na 16.

A ranar Juma’a 24 ga watan Mayu, 2024 Sarki Muhammdu Sanusi II ya karɓi takardar kama aiki a matsayin sarkin Kano na 16, kwana ɗaya bayan gwamna Abba Kabir Yusuf ya sanya hannu kan dokar masarautar Kano ta 2024, wadda ta soke masarautu biyar na jihar.

A shekarar 2019 ne majalisar dokokin jihar Kano ta yi dokar da ta samar da masarautun Kano, Rano, Bichi, Gaya da kuma Ƙaraye, sannan kuma daga bisani gwamnatin jihar ta sauke Muhammadu Sanusi II a msatyin sarkin Kano na 14 bayan zargin shi da rashin biyayya da kuma almundahana da kuɗi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *