Rundunar Yan Sandan jahar Kano, ta gargadi masu rufe manyan hanyoyi Babu gaira Babu dalili, da sunan nadar faifen Bidiyon da za su Sanya a shafukan sada zumunta wato ( Content Creation).
Rundunar ta ce , yin irin wadannan Abubuwa da wasu matasa suka bojiro da su, na rufe hanya suna kwanciya ko yin rawa da kuma Wanka babban laifi ne a dokar kasa ta Nigeria.
Kakakin Rundunar Yan Sandan jahar Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya ce sunga irin wadannan Bidiyon, don haka suke gargadin ma su Yi ko niyyar yin hakan da su daina kamar yadda www.idongari.ng, ta ruwaito.
- Arewa ba cima-zaune ba ne a Najeriya – Ndume
- Dangote zai haɗa kai da kamfanin MRS don sayar da litar fetur naira 935
Haka zalika Rundunar taja hankalin Iyaye su kara Jan kunnen Yayansu, musamman ma su tare Ababen hawa akan hanya , babbar barazana ce , ga rayuwar wasu mutane da hakan zai iya haifar da rasa rayuka da kuma asarar dukiya.
SP Abdullahi Kiyawa, ya kara da cewa, duk Wanda akaga ya rufe hanya, al’umma za su iya Sanarwa a ofisoshin Yan Sanda Mafi kusa , don a kama shi ya fuskanci hukunci.
Ko a kira nambobin waya kamar haka: 08032419754, 08123821575 da 09029292926.