Yan Sanda Sun Gurfanar Da Direban Motar Da Ake Zargi Da Ta Ke Mutane Lokacin Da Suke Sallar Juma’a A Kano.

Spread the love

Rundunar yan sandan jahar Kano, ta gurfanar da Direban Motar nan, mai suna Murtala Abdullahi Azare, bisa zarginsa da hallaka wa Su mutane, a lokacin da suke gabatar da sallar Juma’a a garin Imawa dake jahar.

An gurfanar da Wanda ake zargin ne a gaban kotun majistiri mai namba 4, karkashin jagorancin Rakiya Lami Sani, bisa kunshin tuhume-tuhumen yin tukin ganganci, sanadin mutuwa da kuma rashin Lasisin tuki.

Idongari.ng ta ruwaito cewa an karanto masa kunshin tuhume-tuhumen ya musanta , inda ya shaida wa kotun cewa bai Yi ganganci ba.

Tunda fari Ana zargin sa da ta ke wasu mutane lokacin da suke sallar Juma’a a garin Imawa kan Titin Zaria , inda mutane 12 Suka rasa rayukansu ya yin da wasu da da dama suka jikkata.

Sai dai lauyan da ke Kare Wanda ake zargin Barista A.Y Abdullahi , ya roki kotun ta sanya shi a hannun beli, dogaro da sashi na 168 da kuma 172 ACGL, kotun ta dage zaman ci gaba da shari’ar zuwa Ranar 24 ga watan Yuli 2024, don duba Yi wiwar bayar da beli ko kuma akasin hakan.

Daga karshe mai Shari’a Rakiya Lami Sani , ta bayar da umarnin tsere shi a gidan ajiya da gyaran hali da tarbiya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *