Rundunar yan sandan jahar Kano, ta gurfanar da wasu matasa uku a gaban kotun shari’ar addinin musulinci mai namba 2 dake zaman ta a Kofar Kudu gidan Sarki, bisa zargin da ake yi mu su da satar Dabbobin mutane a Baburan Adaidaita sahu.
Yan sandan sun gurfanar da, Usman Aliyu mazaunin Tukuntawa, Abdulwasi’u Mohd Tudunmaliki da kuma Halifa Isah Sabuwar Gandu, dauke da takaddun tuhuma har guda 20, inda ake zarginsu da hada kai da kuma sata.
An karanto wa wadanda ake zargin takaddar tuhuma daya, mai dauke da zargin satar Akuyoyi 2 ma su kimar kudi naira dubu 120, sai wata Akuyar mai kimar kudi naira dubu 90 wata Akuyar mai kimar kudi naira dubu 70 da kuma kanana guda 3 masu kimar kudi naira dubu 120 sai wata Tunkiya mai kimar kudi naira dubu 70.
Kotun ta aike da su zuwa gidan ajiya da gyaran hali da tarbiya zuwa ranar 14 ga watan Oktoba 2024, don ci gaba da sauraren shari’ar da kuma karanto mu su sauran kunshin tuhumar 19.
- Kotu Ta Bayar Da Umarnin Tsare Mutanen Da Ake Zargi Da Kashe Uban Gidansu Don Su Mallaki Takaddar Fili
- Ana Zargin Wani Matashi Da Cinnawa Kakarsa Wuta A Jigawa.