Yan Sanda Sun Gurfanar Da Matashi Da Ake Zargi Da Kashe Budurwarsa A Kano.

Spread the love

 

Rundunar Yan Sandan jahar Kano, ta Gurfanar da matashin da ake Zargi da hallaka budurwarsa Mai suna Naja’atu Ahmed Yakasai, a gaban kotun majistiri Mai namba 35 dake zaman ta a jahar Kano.

Matashin Mai suna Abubakar Kurna , da Zargin kisan Kai Wanda ya Saba da sashi da 221, bayan karanto masa kunshin tuhumar, sai kotun ta tsaya saboda rashin hurumi.

Idongari.ng, ta ruwaito cewa ana zargin Abubakar Kurna da Halaka budurwarsa Naja’atu Ahmed Yakasai, akan Titin IBB kuma Kafin rasuwarta taje wajensa.

Mai shari’a Huda Haruna, ta dage Shari’ar zuwa ranar 28 ga watan Nuwamban 2024, tare da bayar da umarni ga jami’an gidan ajiya da gyaran hali da tarbiya su ajiye shi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *