Yan sanda sun gurfanar da matashin da ake zargi da Dabawa abokinsa Kwalaba.

Spread the love

Rundunar yan sandan jahar Lagos, ta gurfanar da wani matashi mai suna , Tosin Omotoye, a gaban kotun majistire ta Surulere, bisa zargin sa da daba wa abokinsa kwalaba a sassan jikinsa.

Mai gabatar da kara Insp. Sadiq Adewale, ya shaida wa kotun cewar wanda ake zargin ya aikata laifin ne a yankin Asani Plaza, Ojuelegba Road a Surulere dake jahar a ranar 2 ga watan fabarairun 2024.

Adewale ya kara da cewa Omotoye, ya daba wa Amobi Martins, fashasshiyar kwalabar a a bangaren hagu na fuskarsa da kuma kansam sakamakon musun da ya kaure a tsakanin su.

Wata kotu ta aike da wani Aljani zuwa gidan gyaran hali a Kano

Gwamnatin Najeriya ta gargaɗin NLC kan zanga-zangar da ta shirya yi a ƙasar

Laifin da ake zargin sa da aikata wa ya ci karo da sashe na 173 na dokokin jahar Lagos 2015.

bayan sauraran bangarorin biyu, alkalin kotun Ganiyu Tiamiyu, ya sanya wanda ake zargin a hannun beli, inda wajibi ne ya gabatar da mutane da za su tsaya masa kuma kowanne sai ya ajiye kudi naira dubu dari biyu, haka zalika sai kotun ta ga inda suke zaune.
An dage ci gaba da sauraran shari’ar zuwa ranar 8 ga watan Maris 2024.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *