An gurfanar da wasu ma’aurata a gaban kotun Majistiri mai namba 54, dake Normand’Sland Kano, karkashin jagorancin mai shari’a Ibrahim Mansur Yola, bisa zargi su da hada kai wajen sace wata matashiyar budurwa mai suna Amira Isah Takai mai shekaru 17 da haihuwa.
Wadanda ake zargin sun hada Matheweu Auta da kuma Saira Matheweu mazauna karamar hukumar Tudunwada dake jahar Kano.
A zaman kotun na ranar Laraba mai gabatar da kara Inspecter Fago Lale , ya karanto mu su kunshin tuhumar da ake yi mu su inda dukkaninsu suka musanta zargin.
Sai dai lauyan wadanda ake zargin ya roki kotun ta sanya su a hannun beli , sakamakon sun shigar da kara mai namba K/M1833/2023, a babbar kotun jahar Kano, karkashin jagorancin mai shari’a A’isha Mahmud dan ta dakatar da kwamishinan yan sandan Kano da baturen yan sandan karamar hukumar Tudunwada na ta ke mu su yanci.
Mai shari’a Ibrahim Mansur Yola, ya bayyana cewa shari’ar hakki daban ta laifi ma daban, inda ya ce, lauyan na su a zarbabi wajen nemar mu su belin , domin koda a yan kwanakinnan an kama wasu mutane da zargin satar kananan yara da suke kai su waje a kasarnan kamar yadda Idongari.ng ya ruwaito.
Haka zalika kotun ta ce saboda kare lafiyar wadanda ake zargin, zaman su a tsare ya fi musu kwanciyar hankali.
Mahaifin Budurwar Isah Usman Takai shi ne , ya shigar da korafin sa, wajen yan sanda inda ya zargi miji da matar da sace masa yarinya , kuma kusan kwanaki 43 bai sake ganin ta ba.
Wani lauya dake bibiyar shari’ar Barista Muhammad Inuwa Diso, ya ce, kowa yasan yadda aka samu rahotan satar kananan yara a jahar Kano, har aka samu nasarar kwato wasu a kudancin Nijeriya.
Muhammad Diso ya kara da cewa, ya kamata jama’a su sani cewa, ” duk abinda babbar kotun jahar ke yi suna amfani da tunani da kuma nazari , inda wadanda ake tuhuma, suka nemi daukin ta domin ta bayar da umarnin janye hannun yan sanda daga gudanar da bincike a shari’ar , amma ba su samu odar ba daga kotun.
Sai dai ya ce, an samu wata takaddar dake neman bangarorin shari’ar biyu su bayyana a gaban ta domin jin abunda ya faru” Barista Muhammad Diso”.
” Sannan kotu ta yi amfani da tunanin ta , ta hana su wannan odar, domin da wannan odar ta fito da zata hana jami’an yan sanda gudanar da binciken su, kuma idan suka dauke hannunsu cikin wannan shari’ar ba za a samu damar bayyana a gaban kotun Majistirin da ake shari’ar a yanzu ba”
Sai dai ya ce akwai shaidu da za su gabatar dan tabbatar da zargin da ake yi mu su , dan nema wa yarinyar da mahaifin ta hakkinsu.
Mai shari’a Ibrahim Mansur Yola , ya dage ci gaba da sauraren shari’ar zuwa ranar 23 ga watan Janairun 2023.