Rundunar yan sandan jihar Kano, ta gurfanar da wasu matasa biyu da suka hada Bashir Adamu da Muhammad Bashir, a gaban kotun majistire mai lamba 7, karkashin jagorancin mai Shari’a, Halima Wali dauke da takaddar tuhumar hadin baki don aikata laifi da kuma Yin sata.
Mai gabatar da kara Barista, Farida Wada, ta bukaci kotun ta bayar da dama a karanto musu kunshin tuhumar, Inda kotun ta umarci jami’in ta, Auwalu Jajira , ya karanto musu sannan ya fassara musu da harshen Hausa.
- Gwamnatin Kano ta nemi Tinubu ya kori Aminu Bayero daga fadar Nassarawa
- Buhari ya koma Kaduna da zama bayan shafe shekara 2 a Daura
Wadanda ake tuhumar sun amsa laifukan da Ake Zarginsu da aikatawaJami’an yan sandan ne suka kama su , bisa Zargin satar motoci guda 2 kuma dama an Dade ana nemansu ,Inda suke zuwa daga jihar Plato zuwa nan Kano don yin satar motoci.
A baya dai an yi nasarar kwato motocin sata 2 a wajensu , kotun dai ta bayar da umarnin tsare su a gidan ajiya da gyaran hali da tarbiya zuwa ranar 5 ga watan Maris 2025 don yanke musu hukunci.