Yan Sanda Sun Gurfanar Da Wani Mutum Bisa Zargin Gwada Karfi Da Tsoratarwa Ga Matarsa A Kano.

Spread the love

Babbar Kotun Shari’ar addinin Musulunci da ke zaman ta a unguwar Hausawa Filin Hockey ta bayar da umarnin tsare wani Mutum mai suna ,Abdullahi Muhammad, a Gidan Ajiya da gyaran hali da tarbiya, bisa zargin sa da gwada karfi da tsoratarwa ta hanyar zamantakewar Aure ga matarsa.

Tunda farko Matar ta yi korafin sa, a Ofishin ‘Yan sanda na Gwale, da zargin cin zarafin ta da kuma lakada mata duku kawo wuka Wanda hakan ya sanya aka gurfanar da shi a gaban Kotun.

Mai gabatar da kara ya karanta masa Kunshin Tuhumar da ake yi masa amma ya musanta zargin.

Lauyan dake kare shi a gaban kotun , Barr Umar I. Umar, ya nemi Kotun ta sanya shi a hannun beli dogaro da sashe na 36 na kundin tsarin mulkin Kasa, sai dai mai gabatar da karar Barista Dandago, ya yi suka kan rokon lauyan Wanda ake zargin.

Mai Shari’a Abdullahi Halliru, ya aike da shi gidan ajiya da gyaran hali da tarbiya zuwa ranar Juma’a 14 ga watan Yuni 2024, don ganin lafiyar matar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *