Yan sanda sun gurfanar da wani mutum bisa zargin yaudara da sace Adaidaita sahu a Kano

Spread the love

Rundunar yan sandan jahar Kano ta gurfanar da wani matashi, mai suna Adamu Sani Sharada,a gaban kotun shari’ar addinin musulinci dake zaman ta a unguwar Gama, bisa zarginsa da aikata laifukan yaudara da kuma sace baburin Adaidaita sahu.

Laifin da ake zarginsa da aikata wa ya saba da sashi na 133.

Tunda fari wani mai suna Hassan Usaini ne ya yi korafin sa a wajen jami’an yan sanda da cewer, lokacin da yake gudanar da sana’ar sa, wanda ake zargin ya bayyana masa cewa ya dauke shi domin kai shi gurare da dama dan haka kar ya dauki kowa zai biya shi kudinsa.

Sudan ta Kudu ta haramta giyar da ta hallaka dubban mutane

Kungiyar lauyoyi NBA ta kai karar Hannatu Musawa kan shedar bautar ƙasa NYSC

Sai dai wanda ake zargin ya kai shi wani kantin yan birni daure da gidan gwamnatin jahar Kano, inda ya umarci mai baburin Adaidaita ya sauka ya siyo musu lemo, Maltina da sauran kayayyaki domin su jika makoshin su.

Koda mai babur din ya shiga shagon domin siyo kayayyakin, sai ya gudu da babur din nasa.

A ranar 23 ga watan Janairun 2024 ne, matukin Adaidaita sahun, ya ganshi akan titin gidan zoo Kano, inda ya nemi taimakon jama’a har suka kama shi.

Bayan gurfanar dashi a gaban kotun mai gabatar da kara Aliyu Abidin Murtala, ya karanto masa kunshin tuhumar da ake yi masa inda nan take ya musanta zargin da ake yi masa.

Mai shari’a mallam Nura Yusuf Ahmed, ya bayar da uumarnin tsare shi a gidan a giya da gyaran hali da tarbiya har zuwa ranar 15 ga watan Fabarairun 2024, don dawo wa dashi gaban kotun a ci gaba da shari’ar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *