Jami’an yan sanda sun gurfanar da wani matashi mai suna Usaini Ayuba mazaunin garin Inusawa a karamar hukumar Ungoggo Kano, da takaddun tuhuma guda biyu na zargin siyar wa da al’umma Fulotan da bana sa ba.
An gurfanar da shi ne a gaban kotun shari’ar addinin musulinci dake zamanta a unguwar Kwana hudu , bisa jagorancin mai shari’a Mallam Nura Yusuf Ahmed.
Dubunsa ta cika ne bayan da ya siyar da wasu fulotai ga Isiyaku Sani da kuma Bello Annur mazauna unguwar Dantamashe, kan kudi naira dubu dari tara da hamsin kamar yada idongari.ng, ya ruwaito.
Mai gabatar da kara na kotun Aliyu Abidin Murtala , ya karanto masa kunshin tuhumar da ake yi masa inda ya amsa laifin ba tare da ya wahalar da shari’a ba.
Mai shari’a Mallam Nura Yusuf Ahmed , ya yanke masa hukuncin daurin watanni 9 a gidan a jiya da gyaran hali da tarbiya ko zabin biyan tarar naira dubu hamsin, sannan kuma zai biya wadanda ya cuta kudinsu nan ta ke.
Mai gabatar da karar Aliyu Abidin Murtala ya sake karanto masa kunshin takaddar tuhuma ta biyu, da cewar ya karbi kudin wata matar aure naira dubu dari biyu da hamsin tare da yin alkawarin zai siya mata fili, amma tunda ya karbi kudin ya kashe wayar sa , har ma ya yi kokarin guduwa daga Nijeriya zuwa wata kasa a nahiyar Afrika , inda jami’an tsaro suka yi amfani da kwarewa suka cafke inda suka gurfanar da shi a gaban kotun.
Bayan karanta masa kunshin tuhumar ya amsa laifin sa , sai dai bisa kurewar lokaci Alkalin kotun mai shari’a Mallam Nura Yusuf Ahmed ya dage ci gaba da sauraren shari’ar zuwa ranar 24 ga watan Janairun 2024 domin yanke masa hukunci.
Shugaban masu hada-hadar filaye da gidaje na kasa Alhaji Musa Khalil Hotoro , yaja hankalin al’umma , da su kula wajen siyan fili, gida, rumfar kasuwa , dan kaucewa fada hannun mayaudara.
Ya kuma ce a duk lokacin da irin hakan ta kasance ana kallon masu siyar da filiye duka haka suke, inda ya ce wasu kawai suke bata musu suna.