An gurfanar da wasu Mutane a gaban kotun shari’ar addinin musulinci dake zaman ta, a Unguwar Gama PRP Kana, bisa zarginsu da aikata laifin hada kai da kuma tsoratar da mai kara.
Laifin da ake zarginsu da aikata wa ya Saba da sashi na 120 da 227 na kundin SPCL.
Tunda fari ana zargin Wata mai suna Sadiya Abdulahi , Khalid Yahuza, Bashir Sulaiman da kuma wasu Mutane uku da ba a gabatar da su ba a gaban kotun, wadanda suka tsoratar da mai kara ta Hanyar tilastashi ba su kudi naira dubu dari biyar.
Sai dai ya tura naira dubu Dari uku da hamsin a asusun bankin Bashir Sulaiman, sannan ya tura naira dubu dari da hamsin a asusun bankin Sadiya Abdullahi, bayan sun yi masa barazanar cewar matukar bai ba su wannan kudi ba , za su bata masa suna da cin zarafinsa tare da bayyana wa duniya cewar yana Neman Maza.
Sakamakon hakan ne ransa ya baci , tare da tsorata har ya tura mu su kudaden, amma duk da haka bai tsira ba , amma duk da ya tura wadancan kudaden abun ya zamo tamkar cin Kwan makauniya inda suka Kara neman wasu kudaden , kuma bai yi kasa a gwiba ya shigar da korafinsa a sashin binciken manyan laifuka na CID , inda yan sandan suka gurfanar da Sadiya Abdullahi a gaban kotun.
Mai gabatar da Kara Aliyu Abidin, ya karanto Mata kunshin tuhumar da ake yi Mata , wadda ta musanta zargin.
Sai dai mai gabatar da karar ya shaida wa kotun cewar za su gabatar da shaidu a Ranar 27 ga watan Mayu 2024.
- NSCDC Ta Cafke Likitan Bogi Bisa Zargin Mutuwar Mai Juna Biyu A Osun
- Mun kama mutumin da ya kitsa harin jirgin ƙasa na Kaduna – ‘Yansandan Najeriya