Yan sandan da ke tare da rundunar ‘yansandan Tectical Team, DFI-IRT sun harbe wani dan bindiga da ya yi “kaurin suna wajen garkuwa da jama’a” wanda ke addabar al’ummar kewayen birnin tarayya, Abuja.
Jami’an ‘yan sandan dai sun harbe dan bindigar mai suna Isa Dei-Dei dai yayin wata musayar wuta tsakanin gungunsa da tawagar ‘yan sandan.
Yan sandan Bauchi sun gano Bindigun da aka yasar a kusa da Kogi.
Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan Najeriya, Olumuyiwa Adejobi wanda ya bayyana hakan a ranar Laraba ya bayyana cewa “gungun ‘yan bindigar ya gudu bayan tsinkayen ‘yan sandan to amma sun gudu da harbin bindiga a tare da su”.
Daga karshe Olumuyiwa Adejobi ya yi kira ga al’umma da su kai wa ‘yan sanda rahoto dangane da duk wani mutum da suka gani dauke da harbn bindiga a jikinsa