Yan sanda sun kama ɓarayi 2, sun ƙwato wayoyi 25 a Borno

Spread the love

 

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Borno, ta kama mutum biyu da ake zargin masu ƙwacen wayar salula ne a Maiduguri.

Rundunar ta kuma ƙwato wayoyi 25 da ake zargin na sata ne a hannunsu.

Kakakin rundunar, ASP Nahum Kenneth Daso, ya bayyana cewa Kwamishinan ‘yan sandan jihar, CP Yusufu Mohammed Lawal, ne ya tsara aikin da ya kai ga cafke waɗanda ake zargin.

Ya ce matakin na daga cikin ƙudirin rundunar na tabbatar da tsaron al’ummar jihar.

ASP Daso, ya ce rundunar Kai Ɗaukin Gaggawa (RRS) ce, ta kama mutanen biyu, Ibrahim Abubako da Ibrahim Mohammed, a lokacin da suke kan hanyar Damboa a cikin garin Maiduguri.

A cewarsa, “An same su da wayoyi 25, kuma bayan tambayoyi, sun amsa cewa sun ƙwace wayoyin daga hannun jama’a a ƙauyukan Tashan Alade, Miringa, Kwaya Kusar da Biu da ke kan iyakar Jihohin Borno da Adamawa.”

ASP Daso, ya ƙara da cewa: “Waɗanda ake zargin sun amsa laifinsu kuma ana shirin gurfanar da su a gaban kotu bayan an kammala bincike.

“A yanzu haka, rundunar tana ƙoƙarin mayar wa mutanen da suka ƙwato wayoyin a hannunsu.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *