Yan sanda sun kama barayin Babura,fasa shago, barnata dukiya , fashin waya da kuma ta’ammali da miyagun kwayoyi a Jigawa

Spread the love

 

Rundunar yan sandan jahar Jigawa ta samu nasarar cafke mutane 26, da ake zargi da aikata laifukan, fashin wayar salula, Barayin Babura, Masu barnata kadarori da kuma ta’ammali da miyagun kwayoyi.

Mai magana da yawun rundunar yan sandan jahar DSP Shiisu Lawan Adamu , shi ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da ya aike wa Idongari.ng, a ranar Asabar.


Ya ce sun samu nasarar cafke wadanda ake zargin a sassan jahar sakamakon aiyukan sintiri da rundunar ke yi a koda yaushe.
Cikin wadanda rundunar ta cafke sun hada da wani matashi mai suna Yusuf Badamasi mazaunin unguwar Kofar Yamma a karamar hukumar Babura, da ake zargi da yin amfani da makami tare da aikata fashin waya da kudi naira dubu goma, mallakar Tasi’u Ibrahim.

Rundunar ta kara cafke wani mai suna Mohammad Aliyu, mazaunin jahar Borno, da ake zargi da fasa shago a unguwar Gagulmari tare da satar na’ura mai kwakwalwa da sauran kayayyaki.


Tuni dai rundunar ta gayyaci mai shagon tare da mayar masa da kayan da aka samu a hannun matashin.

Tinubu ya gana da gwamnoni kan taɓarɓarewar tattalin arziƙi da tsaro

Hisbah ta kwace kwalaban giya, ta kama mata masu zaman kansu a Kano

A ranar 19 ga watan Disamba 2023 ,kuma rundunar ta samu korafi daga wajen Yakubu Usman, inda ya shaida mu su cewar ya ajiye Baburinsa kirar Lifan a kofar gida mai kimar kudi naira dubu 700, amma bayan ya fito daga gida sai ya tarar an sace shi.

Bayan samun korafin ne dakarun yan sanda karkashin jagorancin Baturen yan sandan Hadejia, suka shiga farautar wanda ake zargi da aikata laifin satar Babur din.


A binciken da yan sandan suke yi ne suka cafke wani mai suna Abdullahi Muhammad ma zaunin Walawa a karamar hukumar Hadejia dauke da Babur din, har aka samu mukullin komai da ruwan ka wato Master Key da ake zargin da shi yake amfani wajen satar ababen hawan jama’a.

Shiisu Adamu , ya kara da cewa sun kama wani mai suna Najib Binya dauke da na’urar sanyaya daki guda 2 wato AC.

Ana zarginsa da shiga sakatariyar karamar hukumar Kazaure, inda ya yi awon gaba da su, yanzu haka rundunar ta na neman wani mai suna Abba ”C” da ake zargi da hannu a aikata laifin, kuma tuni wanda ake zargin ya amsa laifinsa.


Tawagar rundunar daga Kiyawa,Bamaina da Maigatari, sun kai sumame a maboyar batagari, tare da cafke matasa 22 dauke da miyagun kwayoyi bayan samun bayanan sirri.
Kwayoyin da aka samu a wajen su , sun hada da kwayar Exol guda 254, Diaxapham 123, D-5 Tablets guda 30, Kulin tabar Wiwi 26, Robar Sholusho 26, kwalaben sukudayin 3, Tramadol 2 , Almakashi da kuma katin Chacha.


Hala zalika rundunar ta samu nasarar dawo da Babur kirar Boxer da ake zargin na sata ne.

Rundunar ta ce dukkan wadanda ake zargin sun amsa laifukan su, kuma da zarar an kammala gudanar da bincike za a gurfanar da su a gaban kotu dan su fuskanci hukunci.


Kwamishinan yan sandan jahar AT Abdullahi, ya gargadi batagari da cewa ba su wajen zama a jahar, ko su tuba ko kuma bar jahar baki daya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *