Yan Sanda Sun Kama Bindigu, Wukake Da Miyagun Kwayoyi A Kano

Spread the love

Rundunar yan sandan jihar Kano, ta kama mutane 157 da ake zargi da aikata laifuka mabambanta da suka hada da laifukan fashi da makami, Fadan Daba da barayi da kuma wadanda aka kama da miyagun kwayoyi da kudinsu ya kai sama da naira miliyan dari da hamsin daga ranar 17 ga watan maris zuwa 16 ga watan Afrilun 2025.

Kwamishinan yan sandan jihar Kano, CP Ibrahim Adamu Bakori ne ya bayyana hakan a wani taron manema labarai da ya gudana a shelkwatar rundunar dake unguwar Bompai a yau Laraba.

CP Adamu Bakori ya ce, sun cafke wadanda ake zargi da laifin fashi da makami 24, dilolin kwaya 14, barayin mota 7, barayin Babura 5, barayi 28 da kuma yan daba 79.

Cikin kayayyakin da rundunar ta yi nasarar kwatowa sun hada da bindigu 2 kirar Pistol, bindigu kirar revolver 19 da pistol kirar gida guda 1 sai kuma harsasai.

Haka zalika an kwato motar sata 2, adaidaita sahu 2, Babura 3 da kuma kwayar tramadol ta sama da naira miliyan dari da hamsin 150,000,000:00 sannan an kwato kwalaben madarar sukudayin 22.

An kuma kama Adduna 57, wukake 71, Dan bida 15, Almakashi 7 da kuma kwari da baka guda 1.

Kwamishinan yan sandan ya kara da cewa aikin tsaro ba jami’an tsaro kadai ne ba, abu ne da Yasha al’umma baki daya, inda rundunar ta kara kaimi don fadada sintiri a lungu da sako na fadin jihar Kano.

Dakarun yan sandan sun yi nasarar tarwatsa tawagar wadanda suka kware wajen shigowa da makamai a cikin makon da ya gabata.

A karshe CP Bakori, ya roki al’umma da su ci gaba da basu bayanan sirri don kakkabe aiyukan batagari baki daya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *