Rundunar yan sandan jahar Adamawa ta tabbatar da guntule kan wata mata mai suna Bilkisu Alhaji Idi, a cikin wani Hotel mai suna Happy Guest In dake jahar.
Mai magana da yawun rundunar yan sandan jahar Adamawa SP Sulaiman Yahya Nguroje, ya bayyana hakan a lokacin da yake gana wa da manema labarai.
Idongari.ng, ya ruwaito cewa , wani matum ne ya zo Hotel din, tare da matar har suka kama daki, inda daga bisani ya fito da wata Jaka da ya zo da ita , ya bar Otel kamar yadda wasu daga cikin ma’aikatan suka bayyana.
Bayan haka ne daya daga cikin ma’aikacin taje domin rufe dakunan da aka bari a bude, amma sai ta tarar an guntule kan matar , an yasar da gawar ta a cikin bandaki jini na kwaranya.
Nguroje , ya ce lamarin ya faru ne a ranar 18 ga watan Janairun 2024, da misalin karfe 9:00pm na daren ranar Alhams.
Yanzu haka dai rundunar yan sandan jahar ta cafke ma’aikatan Hotel din su uku, da suka hada da Offer Jacob, Yifarta Caleb da kuma Habibu Isah da ke gadin Hotel din.
Rundunar yan sandan ta gano wani magani da wayar salula a wajen da aka hallaka marigayiyar tare da tafiya da kanta.
Ma’aikaciyar Hotel din ta bayyana wa yan sanda cewar wanda ake zargi da yanke kan matar sunan sa Mozey Adamu , kuma ya bayar da adirieshinsa harda nambar waya, amma ba zata iya gane shi ba, sakamakon ya zo da takunkumin fuska kuma baya bari ma su hada ido da ita.
Auwal Garba, shi ne wanda ya auri marigayiya Bilkisu, amma sakamakon wasu dalilai na zamantakewar aure ya yi mata saki daya a watan daya gabata, ya bayyana rashin jin dadin sa , da samun labarin hallaka matar tasa.
Rohotanni na bayyana cewa hakan ba zai rasa nasaba da aiyukan matsala ba.
SP Sulaiman Nguroje, ya ce yanzu haka kwamishinan yan sandan jahar , ya bayar da umarni gudanar da binciken kwakwaf kan lamarin kuma duk wanda aka samu da laifi za a gurfanar dashi a gaban kotu.