Rundunar ‘yan sandan birnin tarayya wato FCT ta ce ta kama wani mai garkuwa da mutane da ta dade tana nema ruwa a jallo.
Rundunar ta ce mutumin shi ne na biyu a jerin mutanen da suka dade a komarta.
A wata sanarwa da rundunar ta fitar, Sama’ila Wakili da aka fi sani da Habu Ibrahim na daga cikin mutanen da ministan Abuja ya sanya biyan tukwici ga duk wanda ya kama su.
A gaggauta bude shagunan da ba a siyar da magani dake mai Karami Plaza Kano: Kotu
Gwamnan Gombe ya jinjina wa yarinyar da ta lashe gasar karatun Al-Ƙur’ani ta duniya
Sanarwar ta kara da cewa an kama Habu Ibrahim ne a dajin Sardauna Forest da ke yankin garin Toto na jihar Nassarawa mai makwabtaka da Abuja, yayin wani samame da rundunar ta kai.
Daga karshe rundunar ta ce mutumin da ake zargin ya amsa laifukansa inda ya amince shi ne ya kitsa da aiwatar da sace-sacen jama’a da dama a Abujar.