Yan sanda sun kama masu ƙwace waya 35 a Kaduna

Spread the love

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kaduna, ta kama wasu mutum 35 da ake zargi da fashin waya, bayan ta kai samame wasu sassan jihar.

Kakakin rundunar ’yan sandan jihar, ASP Mansir Hassan ne, ya tabbatar da hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Asabar.

Ya bayyana cewa rundunar ƙarƙashin wata tawaga ta musamman sun kai samame wurare daban-daban da nufin kawar da masu ƙwacen waya a jihar.

“Samamen, wanda aka gudanar tsakanin ƙarfe 7 zuwa 11:45, daga ranar Talata zuwa Juma’a, na zuwa ne bayan umarnin Kwamishinan ’yan sanda, Mista Audu Dabigi.

“Samamen ya mayar da hankali ne kan gano wuraren da ake ƙwace waya a birnin Kaduna, inda aka kama mutum 35 da ake zargi, ciki har da mata biyu.

“An samu waɗanda ake zargin ɗauke da muggan makamai, wiwi, da sauran miyagun ƙwayoyi,” in ji kakakin.

Ya kuma ƙara da cewa Kwamishinan ya ba da tabbacin cewa waɗanda aka samu da laifi za a bayyana su kuma a gurfanar da su a gaban kotu.

Sanarwar ta jaddada ƙudurin rundunar na daƙile ayyukan ta’addanci a jihar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *