Yan Sanda Sun Cafke Matar Auren Da Ake Zargi Da Daukar Hayar Matasa Don Su Hallaka Mijinta A Kaduna

Spread the love

Rundunar yan Sandan jahar Kaduna, ta samu nasarar cafke Wata matar aure mai suna Nafisa Salisu, bisa zargin ta da daukar hayar wasu matasa don su hallaka mijinta mai suna Sani Abubakar.

Jaridar Idongari.ng, ta ruwaito cewa, Mijin matar ne ya bata aron kudi naira dubu dari hudu, domin ta yi harkar kasuwanci, amma sai ta kashe kudin ba tare da sanin sa ba.

Nafisa ta bayyana cewa, ta dauki matakin kashe mijin na ta , sakamakon kudinsa da ya nemi ta dawo masa da su, amma ba zata iya fada masa cewar ta kashe su ba.

Matar ta Kara da cewa, ta Fara Neman wani matashi mai suna Tola Rafin Guza Kaduna, don ya hallaka mai gidan nata, inda ya tabbatar Mata cewar ba zai iya ba.

Hukumar Kwastan Ta Kama Muggan Kwayoyi Da Makamai A Tashan Jiragen Ruwa ta Legas

Tola

Rahotanni na cewa, Tolan ya nemo wani mai suna Sulaiman Ibrahim Rafin Guza, inda shi kuma ya ne Monday Magaji , don su hallaka Mijin na ta , akan kudi naira dubu saba’in.

Sai dai Matasan ana zargin sun kai farmaki ga Mijin matar don su hallaka shi, amma ba su yi nasara ba, har aka Kama daya daga cikinsu.

Matar ta bai wa Sulaiman Ibrahim Kafin Alkalamin naira dubu 40, inda za ta cika Masa naira dubu 30, bayan ya kashe Mijin na ta, wadanda aikin na su bai yi nasara ba.

Sulaiman Ibrahim

Yanzu haka dai jama’an Yan sandan suna tsare da matar mai suna Nafisa Salisu, Tola da kuma Sulaiman Ibrahim , sai Monday Magaji da ake nema ruwa a jallo.

Kawo yanzu dai rundunar Yan sandan jahar Kaduna, ta ce komai ba Kan lamarin .

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *