Yan sanda sun kama matashi kan zargin garkuwa da kansa

Spread the love

Rundunar ‘yan sanda jihar Legas ta ce ta kama wani matashi kan zargin ƙaryar garkuwa da kansa.

Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar, Benjamin Hundeyin, ne ya bayyana haka a shafinsa na X, a lokacin da yake tsokaci kan wani saƙo da wani matashi da ke amfani da shafin mai suna @Flacko ya wallafa a shafin.

FlackoT ya wallafa cewa an tsare shi a ofishin ‘yan sanda na Ikeja kan zargin garkuwa da wani mutum da bai san komai game da shi ba.

”Jama’a an tsare ni a ofishin ‘yan sanda. Bani da isasshen lokaci, kuma ban san abin da zan yi ba, wannan ita ce kawai hanyar da zan bayyana wa duniya halin da nake ciki, saboda ku san halin da nake ciki,” kamar yadda matashin ya wallafa.

“Wani ne ya yi ƙaryar garkuwa da kansa, ya kuma buƙaci kuɗin fansa daga wajen mahaifinsa, mahaifin nasa ya kai rahoto wajen ‘yan sanda, inda su kuma suka bibiyi wayata, wllh ba abin da na sani game da batun har sai da na isa ofishin ‘yan sandan”.

Yayin da yake mayar da martani kan saƙon matashin, mai magana da yawun ‘yan sandan na Legas, Hundeyin ya ce binciken ‘yan sanda ya gano cewa wani matashi ne mai shekara 20 ya yi ƙaryar garkuwa da kansa. Inda aka riƙa kira mahifisna da lambobi daban-daban domin neman kuɗin fansa da yadda zai biya kuɗin.

“A ranar Alhamis ne jami’an bincike suka kai samame wani gida a unguwar Lekki inda suka samu Collins da wasu abokansa biyar da suka kwashe kwana 10 suna zaune a gidan”.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *