Yan Sanda Sun Kama Mutane 2 Bisa Zarginsu Da Hannu A Yin Garkuwa Da Mahaifiyar Rarara.

Spread the love

Rundunar ’yan sandan Jihar Katsina ta sanar da cafke wasu mutum biyu bisa zargin hannu a garkuwa da mahaifiyar fitaccen mawaƙin siyasar nan, Dauda Kahutu Rarara.

Mai magana da yawun rundunar a Katsina, ASP Abubakar Sadiq Aliyu ya ce “muna tsare da mutum biyu kan lamarin, muna ci gaba da bincike.”

Tun farko, Kwamishinan tsaro na Jihar Katsina, Nasiru Mu’azu ya ce an sace dattijuwar ce a daren Juma’a a ƙauyen Kahutu da ke Karamar Hukumar Ɗanja.

Mu’azu ya ce waɗanda suka sace matar sun yi hakan ta hanyar bi ta bayan gida, inda suka sace ta ba tare da jami’an da ke tsaron gidan sun sani ba.

Ya kuma bayyana cewa tuni aka tura jami’an tsaro waɗanda suka bazama cikin dazuka domin bin sawun ’yan bindigar.

Aminiya ta ruwaito shaidu a kauyen sun ce da misalin karfe daya na dare ne dandazon ’yan bindiga suka kutsa gidan dattijuwar suka yi awon gaba da ita.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *