Yan Sanda Sun Kama Mutane 3 Bisa Zargin Satar Buhunan Shinkafa 96 A Jahar Nasarawa

Spread the love

Rundunar yan sandan jahar Nasarawa, ta kama wa su mutane 3, bisa zargi su da aikata laifin satar buhunan shinkafa 96, mallakar wani dan kasuwa a karamar hukumar Eggon.

Dan kasuwar ya bayyana cewa ya siyo buhunan shinkafa 700 a jahar Nasarawa, don kai su jahar Abia, amma batagarin su 15,  suka farwa motar kayan akan hanya inda suka wawashe kayan.

Kwamishinan yan sandan jahar CP Umar Nadada, ne ya bayyana hakan a ranar Talata, a lokacin da yake holen wadanda ake zargi da aikata laifuka maban-banta, a fadin jahar.

Wadanda ake zargin sun hada da Auwal Abubakar, Danrimi Mohammed da kuma Habibu Adamu dukkan su mazauna Masaka dake karamar hukumar Karu.

Nadada, ya jinjina wa jami’an yan sandan da suka samu nasarar cafke wadanda ake zargin, a lokacin da suke yunkurin tserewa.

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *