Yan Sanda Sun Kama Mutane 3 Da Ake Zargi Da Halaka Wasu Ma’aurata.

Spread the love

Rundunar yan sandan jahar Abia, ta cafke wasu mutane uku da ake zarginsu da  laifin kisan wasu ma’aurata a yankin Itumbuzo dake karamar hukumar Bende ta jahar.

Mai magana da yawun rundunar yan sandan jahar, Maureen Chinaka, ce ta bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da ta raba wa manema labarai a ranar Asabar.

Chinaka ta ce’’ a ranar 2 ga watan Oktoba 2024 sun samu rahoto daga ofishin yan sanda na Bende, da misalin karfe 8:30pm cewar an samu Ma’auratan da suka hada da, Jacob Udo, mai shekaru 78 da kuma matarsa ,Dorcas Jacob, mai shekaru 73, kwance cikin jini wadanda basa cikin haiyacinsu.

Rahotanni na cewa an yi awon gaba kayayyaki masu tarin yawa a gidan na su, inda yanzu haka  rundunar ta ce ta dukufa wajen gudanar da bincike kan lamarin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *