Yan sanda sun kama mutanen da ake zargi da garkuwa da wani yaro tare da kashe shi a Kano

Spread the love

Rundunar ‘yansandan jihar Kano ta ce ta kama wasu mutum uku bisa zargin garkuwa da wani yaro.

Cikin wata sanarwa da kakakin rundunar yan sandan jahar SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya fitar , ta ce a ranar 8 ga watan Fabrairun da muke ciki ne ta samu rahoto daga wani mutum mai suna Alhaji Rabi’u Abdullahi da ke unguwar Hotoron Fulani cewa wasu mutane sun sace dansa mai suna Abdullahi Sani, inda suka bukaci ya biya naira miliyan hudu don sakin dan nasa.

Sanarwar ta ce daga nan ne kwamishinan ‘yan sandan jihar  CP Muhammed Usaini Gumel , ya umarci sashen yaki da garkuwa da mutane na rundunar ‘yansandan jihar su tabbatar da kubutar da yaron tare da kama maharan.

Cikin binciken farko ne ya kai ga kama wani mutum mai suna Ismail Adamu, mai shekara 22 a unguwar Hotoron Fulani, inda bayan tuhumarsa ne ya amsa laifin da ake zarginsa da aikatawa, yana mai cewa ya hada baki ne wani mutum mai suna Risi da ke unguwar Mariri wajen sace yaron.

Tsarin Firaminista Ne Ya Fi Dacewa Da Najeriya —Aminu Dantata

Tinubu ya gana da gwamnoni kan taɓarɓarewar tattalin arziƙi da tsaro

Ya ce sun boye yaron ne a kauyen Sabuwar Zara, inda suka yanka shi a wuya tare da jefa shi cikin wani masai na wani gidan da ba a kammala ba, sai kuma daga baya suka kira mahaifinsa suka bukaci ya biya naira miliyan hudu kafin su saki yaron.

Sanarwar ‘yan sandan ta kara da cewa ‘yan sanda sun ziyarci wajen da suka boye yaron, inda suka ciro gawarsa daga cikin masan da suka boye shi, tare da kai shi asibitin Abdullahi Wase da ke jihar, inda likitoci suka tabbatar da mutuwarsa.

Binciken ‘yansanda ya kai ga kama wasu mutum biyu a unguwar Hotoron Fulanin da suka dage wajen daidaitawa kan kudin fansar da wadanda suka saci yaron.

‘Yan sandan sun ce za a gurfanar da wadanda ake zargin a gaban kotu da zarar an kammala bincike.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *