Rundunar yan sandan jihar Kano ta samu gagarumar nasarar cafke wasu da ake zargi da aikata laifin fashi da makami da kuma yunkurin kashe wani mai suna Lil-Kesh dake jihar Legas.
An cafke su a ranar 11 ga watan Satumba 2025, unguwar Na’ibawa Kano bayan samun sahihan bayanai, inda suka aikata laifin a jihar Legas sannan suka taho jihar Kano don samun mafaka
Kakakin rundunar yan sandan jihar Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya ce wadanda ake zargin sun hada da Mathew Adewole dan shekaru 25 mazaunin unguwar Na’ibawa da kuma Muktar Muhammad dan shekaru 31 mazaunin unguwa uku Kano.
Binciken farko-farko da jami’an yan sanda suka gudanar, Mathew Adewole, ya tabbatar da cewa sune suka farwa Lil-Kesh, a rukunin gidaje na Bera Estate dake jihar legos a ranar 19 ga watan august 2025, inda suka yi masa fashi tare da yunkurin halaka shi ta hanyar ji masa raunuka a sassan jikinsa.
Haka zalika sun tilasta masa yin taransifa ta naira miliyan biyu da dubu dari da ashirin zuwa asusun bankin Muktar Muhammad.
SP Kiyawa, ya kara da cewa tuni aka mayar da wadanda ake zargin hannun rundunar yan sandan jihar Lagos don fadada bincike kafin a gurfanar da su agaban kotu.
Kwamishinan yan sandan jihar Kano, CP Ibrahim Adamu Bakori, ya yaba da kokarin jami’an da kuma goyon bayan da al’umma suke basu don ganin an tabbatar da zaman lafiya.