Rundunar yan sanda a Abuja, babban birnin Najeriya ta ce ta kai samame wata matattarar miyagu inda ta kama mutum dari uku da bakwai da ake zargi da aikata laifuka.
Kwamishinan yan sanda a Abuja, CP Benneth C. Igwe ne ya jagoranci tawagar rundunar ‘Operation Velvet’ wajen kai samame kan matattarar da ke Gidan Dambe a yankin Dei-Dei zuwa Zuba.
Yayin binciken, an gano bindiga daya da alburusai goma sha biyar a hannun wani da yake ikirarin shi jami’in hukumar tsaro ta farin kaya ne.
KARAN TA WANNAN LABARIN Gobara Ta Ci Ofishin ’Yan Sanda A Kano
Karan ta wannan labarin Hukumar Karbar Koke-Koke Ta Rufe Rumbunan Abinci 5 A Kano
A cewar sanarwar da kakakin rundunar, SP Josephine Adeh ta wallafa a shafin X, sauran kayayyakin da aka gano sun hada da babura da kunshin tabar wiwi da haramtattun kwayoyi da ake zargi mutanen sun sace ne daga hannun mutanen da ba su ji ba su gani ba.
Kwamishinan yan sandan ya ce ana ci gaba da gudanar da bincike kan mutanen da aka kama.
A makon da ya gabata ne aka kaddamar da rundunar ta musamman domin kawo karshen duk wasu miyagun laifuka a Abuja.
Kwamishinan ya kuma gargadi yan sanda kan tatsar jama’ar sannan su nuna kwarewa wajen aiwatar da ayyukansu.