Yan Sanda Sun Kama Wadanda Ake Zargi Da Yin Amfani Da Ankwa Suna Kwacen Wayoyi A Adaidaita Sahu A Kano.

Spread the love

Rundunar Yan Sandan Jahar Kano, ta samu nasarar cafke wasu matasa 8 da ake zargi da aikata laifin kwace wa fasinjojinsu da sauran al’umma wayoyin su na hannu.

An Kama Matasan ne a ranar 23 ga watan Afrilun 2024, lokacin da jami’an yan sanda ke gudanar da aikin sintiri don dakile aiyukan batagari, wadanda suka ga matasa guda 4 a cikin baburin Adaidaita sahu, Bayan an bincike su ne , sai aka samu wayoyin hannu 7, da Ankwa guda 1da kuma Adaidaita sahu.

Binciken farko-farko ya tabbatar da cewa wadanda ake zargin sun bayyana cewa duka wayoyin na sata ne, inda suke amfani da Adaidaita sahun Wajen yi wa Mutane sata da kwace.

Kakakin Rundunar Yan Sandan Jahar Kano SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ne ya bayyana hakan ta cikin Wata sanarwa da ya raba wa manema labarai a Ranar Laraba.

” Wadanda ake zargin sun bayyana cewar suna amfani da baburin Adaidaita sahu, Wajen kwace wayoyin al’ummar” SP Abdullahi Haruna Kiyawa “.

Kayayyakin da aka samu , sun hada da , wayoyin salula guda 9, Ankwa 1, Wuka 1 da kuma baburan Adaidaita sahu guda biyu.

Rahotanni na cewa a Ranar 19 ga watan Afrilun 2024, Rundunar ta samu rahotan cewar an sace wayar wani mutum a gidan Man Matrix dake kan Titin jami’ar Bayero Kano, inda jami’an Yan Sandan suka shiga gudanar da bincike tare da yin amfani da Na’urorin Zamani har aka samu nasarar cafke Mutane uku.

Jaridar Idongari.ng, ruwaito cewa, a Ranar 23 ga watan Afrilu 2024, an samu rahoton wasu batagari a cikin baburin Adaidaita sahu, inda suka kwacewa wani fasinja wayarsa, Bayan samun rahotanni dakarun yan sanda suka bisu har aka Kama mutum daya daga cikin su da wayar salular da aka kwace sai kuma Wata gajeriyar Wuka guda daya.

Yanzu haka dai wadanda ake zargin su 8, suna Babban sashin gudanar da bincike na CID dake Unguwar Bomapai, inda suke Ci gaba da amsa tambayoyin jami’an yan sanda kafin a kammala bincike a gurfanar da su a gaban kotu don su fuskanci hukunci.

Kwamishinan Yan Sandan Jahar Kano, CP Muhammed Usaini Gumel, ya ce rundunar ba zata gajiya ba , wajen ci gaba da kare rayukan al’umma da dukiyoyinsu, inda ya godewa al’ummar Jahar bisa goyon baya da kuma hadin kan da suke bayarwa akoda yaushe.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *