Rundunar yan sandan jahar Kano, ta samu nasarar kwato wasu miliyoyin kudi daga wajen wani mai gadin kamfanin Takalma na Asia Plastic dake unguwar Jogana a karamar hukumar Gezawa dake jahar.
Idongari.ng, ta ruwaito cewa an kama wanda ake zargin mai suna Sadam Habu, dan asalin jahar Adamawa, inda ya fasa ofishin mai biyan kudi, bayan ya saci miliyoyin naira a cikin Akwati sannan ya bankawa ofishin wuta.
Kakakin rundunar yan sandan jahar Kano , SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya ce sun samu labarin faruwar lamarin a ranar 28 ga watan Augustan 2024, inda suka yi nasarar cafke wanda ake zargin a lokacin da yake yunkurin tserewa da kudin.
Rahotanni na cewa kudin da aka samu a cikin akwatin da ya zuba kudin sun haura naira miliyan 20, kuma yanzu haka rundunar ta na ci gaba da gudanar da bincike wanda da zarar an kammala za a gurfanar da shi a gaban kotu.
- Matsalar abinci: Ambaliyar ruwa ta lalata hekta sama da 115,000 a Najeriya
- An Kubutar Da Budurwar Da Aka yi Garkuwa Da Ita A Kano A Dajin Gubuchin Jahar Kaduna.