Rundunar yan sandan jahar Kano, ta kama wasu mutane biyu bisa zarginsu da zuba ruwan rubutu, a cikin wata Rijiya dake kauyen Durmawa, a karamar hukumar Bebeji ta jahar.
jami’in hulda da jama’a na rundunar yan sandan Kano SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ne tabbatar da hakan a sakon muryar da ya aikewa da jaridar www.idongari.ng, a ranar Alhamis.
Ya ce tun a ranar 9 ga watan Disamba 2024, suka samu kiran daga garin Durmawa, da cewar an kama wasu mutane biyu sun zuba wani abu, a cikin rijiyar dake garin.
Bayan samun rahotanne kwamishinan yan sandan jahar CP Salman Dogo Garba, ya tura dakarun yan sanda zuwa wurin, inda aka taho da mutanen guda biyu, inda daya daga cikinsu mai suna, Ado Ahmad, dan shekaru 35 mazaunin unguwar Tudun Murtala a birnin Kano, ya tabbatar da cewa ” Tabbas shi ne ya zuba rubutu a cikin Rijiyar”.
- Gwamnan Kano ya kori Sakataren Gwamnati da Kwamishinoni 5
- Gwamnonin Najeriya sun yi taro a ‘kan dokar haraji’
SP Kiyawa, ya kara da cewa lokacin da aka kamo wadanda ake zargin an samu sauran rubutun a Leda kulli goma 15 da kuma wani kullin magani guda 5.
” ya tabbatar da cewa shi yana kasuwancin magani kuma shi ne ya yi wannan rubutu, sannan yaje wannan Rijiya, ya zuba wani bangare na rubutun don ya samu kasuwa”
Anasa bangaren wanda ake zargin Ado Ahmad, ya ce shi mai bayar da magani ne, na hawan jini, Ciwon Hanta da kuma bawa matan da basa haihuwa, kuma ya zuba rubutun ne don kara bunkasa kasuwancinsa.
A karshe SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya ce yanzu haka wanda ake zargin yana hannun yan sanda ana ci gaba da gudanar da bincike kan lamarin.