Yan Sanda Sun Kama Yan Fashin Da Suka Jiwa Matar Aure Rauni Ta Hanyar Cire Mata Hakori Mai Gwal A Kano

Spread the love

Rundunar yan sandan jihar Kano, ta kama gungun wasu mutane da suke cikin wata kungiyar masu fashi da makami da suka addabi jihar  da makotan jahohi.
Kwamishinan yan sandan jihar CP Ibrahim Adamu Bakori ne , ya bayyana hakan a shelkwatar rundunar dake unguwar Bompai, lokacin da yake yin karin hasken kan nasarar da suka samu.

Ya sun kama wadanda ake zargi da aikata fashi da makami, a unguwar Dorayi Babba Kano, bayan samun lamarin ta’addancin da suka aikata na satar mota da kudin Nijeriya da na ketare kimanin naira miliyan uku da dubu dari bakwai da wayoyin hannu da kuma wasu kayayyaki.

Kwamishinan ya kara da cewa a lokacin da batagarin suke aikata fashin sun jiwa matar gidan Rauni ta hanyar cire mata hakori mai dauke da Gwal a jiki.

Bayan faruwar lamarin jami’an yan sandan Dorayi , sun yi nasarar kama mutum daya daga cikin yan fashin , inda tawagar runduna ta musamman suka kai daukin gaggawa tare kamo mutane 8 a wurare dabam-daban  da suka hada Abuja, Kaduna da kuma Kano.

Wadanda ake zargin sun hada da Abubakar Aminu mai shekaru 22, Aliyu Aliyu mai shekaru 23, Abubakar Usman mai shekaru 22, Suleiman Sani mai shekaru 20, Yusuf Yusuf mai shekaru 17, Abdurrahaman Aliyu mai shekaru 23, Salisu Hussaini mai shekaru 17, Suleiman Abdullahi mai shekaru 20 da kuma Abdulmudallib Sa’ad mai shekaru 24.

Kayayyakin da aka kwato daga wajen su,sun hada da Bindiga kirar double barrel da harsasai 18, Bindiga kirar bature  Falcon pistol da bindiga kirar Phoenix oistol da abin yanka karfe da adduna 2 da wukake msu kaifi 4 da fitilu 3 da Jar Mota Toyota Corolla LE wacce suke zuwa fashi da ita da kuma wayoyi guda 2.

Dukkan wadanda ake zargin sun amsa cewa sune suka addab jahohin Kaduna da Abuja da Kano, kuma sune suka aikata fashi a unguwar Jakada Doroyi Kano.

Kwamishinan yan sandan jihar CP Ibrahim Bakori, ya tabbatar da cewa Operation kukan da suka kaddamar ya taka muhimmiyar rawa wajen rage laifukan a fadin jihar kamar sata da kwacen waya a titi da harkar fadan dabaduk sun takaita.

Ya kuma ya bawa jami’an yan sandan da suka jagoranci aikin bisa nuna kwarewa da jarumta, inda ya yi kira ga sauran jami’an su ci gaba da nuna kokarinsu .

A karshe ya godewa al’ummar jihar bisa addu’o’i da kuma goyon bayan da suke ba su a koda yaushe.

 

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *