Yan Sanda Sun Kama Yan Jagaliyar Wani Jigon Siyasa Bisa Yunkurin Tada Riciki A wajen Rantsar Da Sabbin Kwamishinoni A Kano

Spread the love

Rundunar yan sandan jahar Kano ta samu nasarar cafke wasu Yan Jagaliyar siyasa 8, wadanda suke yawo a ofisoshin yan siyasa , bisa zarginsu da yunkurin tada riciki, a wajen rantsar da sabbin kwamishinonin da gwamnatin jahar Kano ta yi a ranar Alhamis.

Kakakin rundunar yan sandan jahar Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ne ya tabbatar da hakan ga jaridar Idonagari.ng.

Kwamishinan yan sandan jahar Kano, CP Muhammed Usaini Gumel, ya gargadi ma su daukar nauyin yan Jagaliyar, don su haifar da matsalar da zata shafi tsaron jahar Kano, da su sani cewar  rundunar ta shirya tsaf domin kama mutum tare da gurfanar da shi a gaban kotu don ya fuskanci hukunci.

A ranar Alhamis din nan gwamnan jahar Kano, Engr. Abba Kabir Yusuf, ya  rantsar da sababbin kwamishinoni guda hudu, da suka hada da Mustapha Rabi’u Musa kwankwaso, a matsayin kwamishinan ma’aikatar matasa da wasanni, Abduljabbar Garko a matsayin kwamishinan kasa da safayo na jihar kano, Shehu Aliyu Yarmedi a matsayin kwamishinan aiyuka na musamman da kuma Adamu Aliyu Kibiya , a matsayin kwamishinan kasuwanci da masana’antu na jihar Kano.

Kakakin rundunar yan sandan jahar Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya ce yanzu haka wadanda ake zargin suna babban sashin gudanar da bincike na manyan laifuka dake Bompai, don fadada bincike akan su kamar yadda jaridar idongari.ng ta ruwaito.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *