Yan sanda sun kashe masu taimaka wa yan fashin daji da makamai

Spread the love

Rundunar yan sandan Najeriya ta ce ta halaka wasu rikakkun yan bindiga da suka addabi Abuja da Kaduna da Kogi da Nassarawa a kokarin da jami’anta ke yi na murkushe masu garkuwa da yan bindiga daga kasar.

Ta ce jami’anta karkashin rundunar FID-IRT ta musamman ne suka kai samame kan maboyar yan bindigar a Gitata da ke jihar Nassarawa.

Wata sanarwa da kakakin hedikwatar rundunar yan sanda, ACP Olumuyiwa Adejobi ya fitar ta ce an gano bindigogi kirar AK47 da muggan makamai da leda makare da alburusai.

Ba mu muka hana Hafsat Chuchu kin yin Magana agaban kotu ba: Barista Haruna Magashi

An Kama Mai Garkuwa Da Mutane Yayin Karɓar Kuɗin Fansa A Taraba

Rundunar ta ce mutanen da aka halaka suna da hannu wajen kai wa yan fashin daji makamai.

Rundunar ta ce za ta ci gaba da daukan matakai na kawar da masu aikata miyagun laifuka tare da tabbatar da doka da oda da kuma zaman lafiya a fadin Najeriya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *