Rundunar ‘yan sandan birnin tarayya Abuja sun ce sun kuɓutar da wani mutum da aka yi garkuwa da shi a kan titin zuwa filin jirgin saman birnin.
A ranar Juma’a ne masu garkuwar suka sace mutumin a lokacin da yek tuƙa motarsa zuwa gida bayan tashi daga wurin aiki.
Mutumin mai suna Sulaiman Sabo na tare da matarsa a lokacin da lamarin ya faru, inda maharan suka ƙwace motar da suke cikin.
To sai dai a ranar Lahadi kwamishin ‘yan sandan birnin Abuja, CP Haruna Garba, ya sanar da kuɓutar da Sabo
Yayin da yake jawabi a taron manema labarai a shalkwatar rundunar, CP Garba ya ce jami’an ‘yan sanda da ke aiki a ofishin ‘yan sanda na Iddo ne suka kuɓutar da shi a ƙauyen Sauka.
Ya kuma ce an kama mutum guda, mai suna Muhammed Abel, mazaunin jihar Kogi da ake zargi na da hannu a sace mutumin.
Kwamishin ‘yan sandan Abujan ya kuma jami’ansu sun ƙwato bindiga guda tare da alburusai daga mutumin.
A baya-bayan nan jami’an tsaron ƙasar musamman a Abuja na matsa ƙaimi wajen yaƙi da masu garkuwa da mutane don neman kuɗin fansa.
Ko a ranar Juma’a ma ‘yan sanda sun kuɓutar da wani mutum a Kaduna, bayan da masu garkuwar suka sace shi a Abuja, inda suka nufi Kano da shi.
Haka kuma a ranar Asabar ma jami’an tsaron ƙasar sun sanar da kuɓutar da ‘yan matan nan biyar daga cikin shida da suka sace a yankin Bwari da ke Abuja, babban birnin tarayyar Najeriya.
Hakan na zuwa ne bayan kashe ɗaya daga cikin ‘yan matan mai suna Nabeeha kimanin mako biyu da suka gabata.