Yan sanda sun kubutar da yan uwan Nabeeha da masu garkuwa da mutane suka hallaka

Spread the love

Rundunar ‘yan sandan Nijeriya ta ce jami’an tsaro sun kubutar da ‘yan matan nan biyar da ke hannun masu garkuwa da mutane bayan ‘yan bindiga sun kashe ‘yar’uwarsu wato Nabeeha Al-Kadriyar.

An sace ‘yan matan shida ne da mahaifinsu ranar 2 ga watan Janairun da muke ciki a gidansu da ke Bwari a Abuja.

Sai dai daga bisani ‘yan bindigar sun saki mahaifinsu sannan suka bukaci ya nemo N60m a matsayin kudin fansa.

Sanarwa da jami’ar hulda da jama’a ta rundunar ‘yansanda, reshen birnin tarayya, Abuja, Josephine Adeh ta fitar na cewa: “Bayan matsa kaimi na sashen yaki da satar mutane na rundunar ‘yansanda tare da hadin gwiwa da jami’an sojin Najeriya game da harin da masu garkuwa da mutane suka kai kan unguwar Zuma 1 na yankin Bwari a ranar 2 ga watan Janairun 2024, ‘yansandan yankin Birnin Tarayya sun samu nasarar ceto wadanda abin ya rutsa da su.”

Sanarwar ta kara da cewa “tuni aka hada su da ‘yan’uwansu.”

Sai dai sanarwar ba ta yi karin bayani kan ko an yi artabu tsakanin jami’anta da masu garkuwa da mutanen ba ko kuma a’a.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *