Yan Sanda Sun Manta Hularsu A Motar Dalibi Bayan Karɓar Cin Hancin N99,000

Spread the love

Wani dalibi mai suna Olawale Ayomide ya zargi wasu ’yan sanda da ke aiki a ofishin Igbeba da ke yankin Ijebu Ode a jihar Ogun da tatsar Naira 99,000 daga hannunsa ba bisa ka’ida ba.

Ayomide ya ce lamarin ya faru ne a ranar Talata, inda ya ce ɗaya daga cikin ’yan sandan da ake zargi ya manta hular aikinsa a cikin motar bayan sun aikata abin da ake zarginsu da yi.

A cewarsa, ’yan sandan sun tsayar da shi ne a lokacin da yake tafiya daga Shagamu zuwa Ijebu-Ode a cikin motar mahaifiyarsa, inda suka zarge shi da tuƙi ba tare da lambar mota ba.

Ya ce duk da ya bayyana musu cewa motar ta mahaifiyarsa ce kuma tana cikin tsarin yin rajista, ’yan sandan sun ƙi sauraron bayaninsa, suka ce sai ya bi su zuwa ofishinsu.

“Ina kan hanyata daga Sagamu zuwa Ijebu-Ode ne lokacin da muka haɗu da wasu ’yan sanda a hanya. Sun tsayar da mu, suka ce mu fito daga mota ni da abokina. Motar ta mahaifiyata ce, kuma tana cikin tsarin yin takardun rajista,” in ji Ayomide.

“Ba tare da sun faɗa mana laifinmu ba, sai suka shiga motar suka ce mu bi su zuwa ofishinsu. A hanya muka tambaye su laifinmu, sai suka ce muna tuƙi ba tare da lambar ba. Mun yi ƙoƙarin bayyana musu halin da ake ciki, har ma muka nemi mu kira mahaifiyata don ta tabbatar da mallakar motar, amma suka ƙi, suka nace sai sun kai mu ofis.”

Ayomide ya ƙara da cewa a hanya, ’yan sandan sun nemi ya biya naira miliyan ɗaya kafin su sake su, kuma sun yi barazanar kwace motar idan ya ƙi biyan kuɗin.

“A ƙarshe suka ce mu ajiye motar kusa da ofis, suka ce za su karɓi naira 100,000. Tun da ba za su bar mu ba. Sai na kira dillalin wayata na ce masa zan sayar da wata wayata don ya turo min kuɗin. Bayan na samu saƙon shigowar kuɗi, sai suka kai ni wajen mai PoS, inda na tura musu naira 99,000.”

Bayan sun bi umarnin ’yan sandan, an sako su.

Amma daga bisani, Ayomide da abokinsa sun gano hular ɗaya daga cikin ’yan sandan a kujerar bayan motar lokacin da suka isa gida.

 

“Mun gano hular ɗan sanda a kujerar bayan motar a gida. Mun faɗa wa mahaifiyar Ayomide abin da ya faru,” in ji Ifeanyi.

Da aka tuntubi mahaifiyar Ayomide, Misis Omolabake, ta tabbatar da cewa motar tata ce, kuma ta nuna rashin jin daɗinta kan abin da ya faru.

“Na ga hular a cikin mota, na tambayi ɗana inda ya samo ta. Da farko bai so ya faɗa min abin da ya faru ba sai da na matsa masa. Wannan ba yi dadi ba. Sunana yana cikin takardun motar. Muna cikin tsarin neman lambar motar. Ban ji daɗi ba lokacin da aka faɗa min abin da ya faru.

“Na san abin da suka yi ba daidai ba ne, kuma haka lamarin ya kare. Mijina ba ya nan yanzu, ina jiran dawowarsa kafin mu je ofishin ’yan sandan. Dole ne su mayar da kuɗin da suka karɓa kuma su goge bidiyon da suka ɗauka.”

Duk kokarin wakilinmu na jin ta bakin Kakakin ’Yan Sanda jihar ta Ogun, Omolola Odutola, ya ci tura, domin ba ta amsa kiran waya ko amsa rubutaccen sakon da aka tura mata ba, har zuwa lokacin hada wannan rahoton.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *