Yan Sanda Sun Mayar Da Baburin Adaidaita Sahun Da Aka Sace Tare Da Kama Wadanda Ake Zargi A Kano.

Spread the love

 

Rundunar yan sandan jahar Kano, ta yi nasarar kwato wasu baburan adaidaita sahu na sata guda biyu, bayan samun sahihan bayanan sirri kan maboyar wadanda ake zargi a karamar hukumar Danbatta ta jahar.

Kakakin rundunar yan sandan jahar Kano, SP Abdullahi Haruna ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da ya rabawa da manema labarai a ranar Alhamis.

SP Kiyawa, ya ce a ya yin sumamen an cafke mutane biyu da ake zargi wadanda suka hada da , Ado yusuf mai shekaru 40 da kuma Rabi’u Suleiman dan shekaru 35, tare da kwato baburan adaidaita sahun sata daga hannunsu , kuma a lokacin bincike sun gaza bayar da gamshasshiyar amsa kan baburan.

Wannan nasarar na zuwa ne , bayan taron manema labarai da rundunar yan sandan ta yi, a ranar 10 ga watan Disamba 2024, inda daya daga cikin mamallakin baburin adaidaita sahun mai namba KGM 246VC, ya shaidawa rundunar a ranar 17 ga watan Disamba 2024 , cewa wadanda ake zargin sun fesawa matukin adaidaita sahun kwaya, sannan suka sace Adaidiata sahun.

 

Ya kara da cewa, an garzaya da matashin zuwa asibitin kwararru Murtala Muhammed, inda daga bisani aka mayar da shi , makarantar gyaran tarbiya Kiru ( Reformatory Institute Kiru) inda aka duba lafiyarsa sannan aka sallame shi.

Kwamishinan yan sandan jahar Kano, CP Salman Dogo Garba, ya bayar da umarnin gudanar da bincike, kafin a gurfanar da wadanda ake zargin a gaban kotu don su fuskanci hukunci.

Haka zalika rundunar ta bukaci al’umma musamman wadanda suka taba fadawa tarkon batagarin, su kai korafin su ofishin kakakin rundunar yan sandan jahar, dake unguwar Bompai ko kuma a kira nambar waya 07038874340, ko kiran waya kan wani zargi da ba amince da shi ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *