Rundunar yan sandan jihar Kano, ta tabbatar da mutuwar wani matashi mai suna Musa Nuhu, mazaunin unguwar Dorayi Jakada, bayan Yasha dukan kawo wuka lokacin da ake zargin yaje wani gida yin fashi da makami.
Kakakin rundunar yan sandan jihar Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na facebook.
Kiyawa, ya ce matashin ya shiga gidan mutanen ne da wuka don ya yi musu fashi, kuma har yayi wa mata 2 raunuka inda wani namiji dake cikin gidan yayi kukan Kura kuma yayi kansa.
Sanadiyar hakanne suka fafata, har aka garzaya da matashin da ake zargi zuwa asibiti, inda daga baya lokitoci suka tabbatar da rasuwarsa.