Yan Sanda Sun Tabbatar Da Mutuwar Mutane 10 A Wajen Rabon Tallafin Abinci A Abuja

Spread the love

Shugaban Najeriya Bola Ahmad Tinubu ya soke ayyukan da ya tafi yi a jiharsa ta Legas domin karrama wadanda suka mutu sakamakon turmutsutsin da ya janyo hasarar rayuka a Abuja da jihar Anambra.

Aƙalla mutum 10 sun mutu, ciki har da ƙananan yara, yayin da da dama suka samu raunuku sakamakon wani turmutsutsu da ya faru a cocin Catholic da ke unguwar Maitama a Abuja.

Cikin wata sanarwa da rundunar ‘yansandan birnin Abuja ta fitar, ta ce cikin waɗanda suka mutu har da ƙananan yara huɗu, yayin da mutum takwas suka samu munanan raunuka, kuma suke karɓar magani a asibiti.

Can ma a jihar Anambra da ke kudu maso gabashin ƙasar rahotonni na cewa wasu mutane sun mutu bayan wani turmutsutsu da aka samu a wajen rabon tallafi a jihar a ranar ta Asabar.

Sanarwar da fadar shugaban Najeriyar ta fitar ta ce shugaban ya soke kallon wasan kwale-kwale da aka tsara zai yi a Ikoyi. Sannan ya yi wa mamatan addu’a tare da fatan murmurewa ga waɗanda suka jikkata.

Yan Najeriya na fama da matsin rayuwa sakamakon matakan da gwamnatin Tinubu ke ɗauka kan tattalin arziki waɗanda suka kai ga janye tallafin man fetur wanda kuma ya haddasa tsadar kayan abinci da sufuri.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *