Rundunar ƴan sandan jihar Kano ta ce masu Garkuwa da mutane su biyun da ta kama a dajin Ɗansoshiya da ke kwanar Ɗangora a ƙaramar hukumar Ƙiru a jihar sun rasu.
Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ƴan sandan SP Abdullahi Harun Kiyawa ne ya sanar da hakan a shafin sa na sada zumunta a cikin daren Asabar 09 ga watan Nuwamban 2024.
Tun dai da safiyar Asabar ne rundunar ta ce ta cafke mutane biyun da ta ke zarginsu da shiga jihar Kano, domin yin garkuwa da mutane tare da neman kuɗin fansa.
- Yadda mutanen gari suka yi artabu da Lakurawa a Kebbi.l
- SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya bayyana cewa, an kama mutanen ne a garin Kwanar Dangora, kuma, suna hannun ‘yan sanda domin fadada bincike, ko da ike yanzu haka tuni suka riga mu gidan gaskiya.
Majiyar Dala FM Kano ta rawaito cewa SP Kiyawa ya kuma ƙara da cewa, yanzu ta’addancin satar mutane ba za ta yi tasiri a Jihar Kano ba da yardar Allah’.
Mai magana da yawun rundunar ƴan sandan na Kano, ya kuma gode wa al’ummar jihar bisa addu’o’in da suke yi a kullum.
Tuni dai Kiyawa ya wallafa hotunan gawar mutanen biyu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne a shafin sa na Facebook.