Yan Sanda Sun Tabbatar Da Rasuwar Mutane 4 A Turmutsutsin Rabon Zakka A Bauchi.

Spread the love

Rundunar yan sandan jahar Bauchi ta tabbatar da mutuwar mutane hudu a yayin karbar Zakkar da kamfanin Shafa Holdings plc, ke rabawa a ranar lahadi.

Kakakin rundunar yan sandan jahar Bauchi SP Ahmed Mohd Wakil, ne ya tabbatar da hakan ga manema labarai.

Ahmed Wakil, ya ce bayan faruwar lamarin sun garzaya wajen tare hakurkurtar al’umma da su kasance masu hakuri a duk lokacin da wani abu ya faru.

Wata mai suna Na’ima Abdullahi mai shekara 17, ta jikkata a wajen rabon zakkar, wanda yanzu aka kwantar da ita a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa da ke Bauchi.

Yan sanda sun tarwatsa dandazon jama’a da ke wajen domin karbar zakka, tuni rundunar ta jibge motocin dakarunta domin tabbatar da tsaro a yankin.

Kawo yanzu dai babu wata sanarwa a hukumance da kamfanin ya fitar game da faruwar lamarin.

NDLEA ta ja hankalin mutane kan sabuwar hanyar da ake ha’intar matafiya da ita

An ƙara kashe ‘yansandan Najeriya shida a jihar Delta

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *