Yan Sanda Sun Tabbatar Da Rasuwar Mutane 5 cikin 20 Da Kwale-kwale Ya Kife Da Su A Jigawa.

Spread the love

Wani kwale-kwale ya kife da fasinjoji 20 a jahar Jigawa , a lokacin da suke kokarin tsallaka, kogin Gamoda zuwa kauyen Nahuce a karamar hukumar Taura ta jahar.

Kakakin rundunar yan sandan jahar Jigawa DSP Shiisu Lawan Adamu, ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da aike wa da manema labarai a ranar Alhamis.

Sanarwar ta ce wata majiya ta tabbatar da cewa lamarin ya faru ne da misalin karfe 12:00pm na rana, inda mutane 5 suka rasa rayukansu.

Idongari.ng, ta ruwaito cewa bayan samun faruwar lamarin ne, aka tura tawagar yan sanda hadin gwiwa masunta domin aikin ceto.

Rundunar ta bayyana sunayen mutanen da suka rasu wadanda suka hada da , Abdurra’uf Mohd mai shekaru 12,  Suleman Ali mai shekaru 20, Shafiu Mohd dan shekaru 25,  Ado Nafance dan shekaru 75 da kuma Alasan Mohd ‘dan shekaru 16dukkan su mazauna karamar hukumar Taura dake jahar.

Yanzu haka dai ana ci gaba da aikin ceton sauran mutane 15 da ba a gani ba.

Kwamishinan yan sandan jahar Jigawa, CP AT Abdullahi , ya jajantawa iyalan wadanda suka rasu, tare da yi mu su addu’ar Allah ya jikan su.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *