Yan Sanda Sun Tsunduma Yajin Aiki Saboda Far Musu Da Ake Yi A Bangladesh

Spread the love

Ƴan sanda a Bangladesh sun tsunduma yajin aiki saboda abin da suka ce ƙaruwar hare-haren ramuwar gayya da ake kai masu, kwana ɗaya bayan da tsohuwar Firaiminista Sheikh Hasina ta yi murabus.

Sun ce ba za su koma aiki ba har sai an tabbatar da tsaron duka jami’ansu.

Wata sanarwa daga wata ƙungiyar ƴan sanda ta nemi afuwa kan ƙarfin da aka yi amfani da shi kan masu zanga-zanga a makonnin baya-bayan nan.

Rahotanni sun ce hankali ya kwanta a Dhaka, babban birnin ƙasar sai dai akwai rahotannin sace-sace da kashe-kashe a sassan ƙasar.

Shugaban ƙasar, Mohammed Shahabuddin na tattaunawa da shugabannin ɗalibai da suka jagoranci zanga-zangar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *