Rundunar ƴansanda a jihar Kano da ke Najeriya ta ce ta kama mutum 326 bisa zargin su da hannu a yamutsin da aka samu lokacin zanga-zangar matsin rayuwa a ranar Alhamis.
Rundunar ta ce cikin mutanen da ta kama akwai mata, da maza da kuma ƙananan yara.
Haka nan sun bayyana cewa an ƙwace bindiga ƙirara AK47.
Zanga-zangar lumanan da matasa suka shirya a faɗin ƙasar ta rikiɗe zuwa rikici a wasu jihohi, lamarin da ya kai ga sanya dokar ta ɓaci a jihohi biyar.
A Kano masu zanga-zanga sun ɓalle shaguna da ɓarnata kayan gwamnati a lokacin da lamarin ya yamutse.
Saurari karin haske daga bakin mai magana da yawun rundunar yan sandan Kano SP Abdullahi Haruna Kiyawa.