Rundunar yan sandan jahar Kano, ta zargi wasu daga cikin mutanen unguwannin Dorayi, da karbo mafi yawan matasan da aka kama da laifukan Daba a jahar.
Kakakin rundunar yan sandan jahar Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ne ya bayyana hakan a shafin na Facebokk, a ranar Laraba.
SP Kiyawa, ya ce matasan da suka dawo harkar Daba, sun kama su tare da gurfanar da su a gaban kotu, amma wasu daga cikin mutanen yankin suka tsaya mu su, tare da karbar su a matsayin beli, sai dai rundunar ba ta bayyana suneyen mutanen ba.
A karshe Abdullahi Kiyawa, ya ce nan gaba kadan za su yi karin haske kan wannan zargi da rundunar yan sandan jahar Kanon ke yi wa wasu daga cikin mazaunin unguwannin Dorayi.
- Nyesom Wike Ya Zargi Wasu Jami’an Gwamnati Da Yi Wa Tsarin Filayen Abuja Zagon Kasa.
- Kotu Ta Bai Wa DSS Damar Tsare Wani Dan ISIS’ Tsawon Kwanaki 60